Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn yi radin sunan jaririn nan da ya kusa rasa hannun sa...

An yi radin sunan jaririn nan da ya kusa rasa hannun sa a asibitin Aminu Kano

Date:

Kabir Bello Tukur

 

Anyi raɗin sunan yaron nan da ake zargin sakacin wani likita ya kusa illatawa hannu a Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano a jiya Alhamis.

 

Yaron da aka raɗawa suna ‘Shamsuddeen’ na cigaba da jinyar hannun sa a ɓangaren jarirai na asibitin, wanda yau yake cika kwanaki 8 cif a duniya.

 

Tuni dai kwamitin ladabtarwa da hukumar asibitin ta kafa ya gana da likitan da yayi aikin, tare da yin zama da mahaifin jaririn don jin ta bakinsa.

 

Zuwa yanzu dai, ana dakon ganin irin matakin da kwamitin zai bada shawarar ɗauka, bayan gamsuwa da yayi cewa akwai sakaci a lamarin, kamar yadda wata majiya ta shaidawa Premier Radio.

 

A makon da muke bankwana da shi ne wannan al’amari ya faru, bayan da wani likita a asibitin Aminu Kano, ya dauki jinin jaririn, sannan ya manta tsirkiyar da ya daure hannun har na tsawon awanni, abinda yayi sanadin fara rubewar hannun.

 

Ko da yake a baya, hukumar asibitin ta bayyana shakku kan yuwuwar hannun ya mike a nan gaba, to amma ya sami sauki sosai.

 

Tun bayan fitar labarin da Premier Radio ta wallafa, batun ya karade kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...