Saurari premier Radio
41.5 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniDuk da Neymar, Messi da Mbappe PSG ba zata iya lashe Champions...

Duk da Neymar, Messi da Mbappe PSG ba zata iya lashe Champions League ba–Larque

Date:

Tsohon Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon ta Paris Saint-Germain Jean-Michel Larque ya ce abu ne Mai wahala Kungiyar ta iya lashe Champions League duk da Lionel Messi, Kylian Mbappe da Neymar da take da su.

 

Ya ce Yan wasa ukun yadda suke kokarin zura kwallo to ba su da karfin da zasu iya tsare bayan kungiyar.

 

Dan kasar Faransa ya kara da cewa rashin karfin kungiyar a matakin baya shi ne babban kalubale da PSG din ke fuskanta.

 

“Idan ka kalli Sergio Ramos shi ka dai kokarinsa ba zaka iya cewa ko da yaushe ne ba, amma ba zan zargi cewa ba ya kokari a Kungiyar ba” a cewar Larque a zantawarsa da kafar PSG.

 

Ya kara da cewa “Ba kuma zance kungiyar ba tada Yan wasan baya masu nagarta ba, sai dai gasar Champions League da ban take kuma a PSG matuka a kwai gyara”

 

Kawo yanzu dai Yan wasa ukun wato Lionel Messi ya zura kwallaye 8 da taimakwa aka ci 10, Neymar kuwa ya ci kwallaye 10 da taimakawa a kaci 10.

 

Sai kuma Kliyn Mbappe a kakar wasanni ta bana ya ci kwallaye jumulla 13.

Latest stories

Ýan Houthi sunyi iƙirarin kai hari kan wasu jiragen ruwa hudu.

'Yan Houthi na kasar Yemen, sun yi ikirarin kai...

Zamu kawo ƙarshen wahalar man fetur gobe laraba- NNPCL.

Kamfanin mai na kasa, ya tabbatar da cewa, gobe...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...