Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeFIFAMakomar Super Eagles a gasar cin kofin Afrika | Premier Radio |...

Makomar Super Eagles a gasar cin kofin Afrika | Premier Radio | 27.03.2023

Date:

Suhaib Auwal Gwagwarwa

A yammacin yau Litinin ne kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagles za ta fafata da kasar Guinea-Bissau a wasa na biyu na neman cancantar zuwa gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2023.

Guinea-Bissau ta doke Nigeria da ci daya mai ban haushi a wasan farko da aka fafata a filin wasa na MKO Abiola dake babban birnin tarayya Abuja.

Tuni dai tagawar Nigeria ta isa kasar ta Guinea-Bissau, domin buga wannan wasa mai hatsari ga kasar.

Sabon mai horas da Super Eagles Jose Peseiro na cikin tsaka mai wuya kasancewar kasar nan ba ta yi nasara a wasanni hudu a jere ba, kuma idan Nigeria bata yi nasara a wannan wasan ba, akwai yiwuwar za ta kasa samun tikitin zuwa gasar ta cin kofin Afrika.

A nan kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria NFF Ibrahim Gusau ya koka kan yadda manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar ke kasa tabuka abun azo a gani a manyan wasanni, yana mai bayyana cewa zasu sake yin duba kan matakan daukar ‘yan wasa a kungiyoyin.

A jawabin da ya yi wa Super Eagles gabanin wasan su na biyu da Guinea-Bissau Ibrahim Gusau ya ce dole ne ‘yan wasan su kara zage dantse wajen ganin an samu nasara a wasanni masu zuwa.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...