Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniNLO:A Karon farko jihar Kano zata karbi bakuncin bude gasar matasa ta...

NLO:A Karon farko jihar Kano zata karbi bakuncin bude gasar matasa ta kasa

Date:

Masu shirya gasar matasa ajin kwararru ta kasa Nationwide League One (NLO), sun sanar da jihar Kano ce zata karbi bakuncin wasan farko na bude gasar ta kakarar wasannin 2022/23.

Sabon jamiā€™in yada labaran gasar ta kasa Abdulgafar Oladimeji ne ya bayyana hakan a ranar a wani taron manema Labarai da ya gudana a nan Kano.

Abdulgafar ya ce za a fara gasar a ranar 04 ga watan Mayu a manyan cibiyoyin kasar nan daban-daban da aka ware.

Inda akalla ake da shiyya shiyya guda 8 da zasu karbi bakuncin gasar, kuma jihar Kano nada rukuni biyu da za a fafata a gasar.

Kuma an ware filayen wasanni na Sani Abacha dake Kofar Mata, dana Kano Pillars dake unguwar Sabongari.

Haka zalika wasu cikin cibiyoyin da za a gudanar da gasar sun hada da filin wasa na Ahmadu Bello dake Zaria, dana Pantami dake jihar Gombe.

Sauran sune filin wasa na Karkanda dake Katsina, da kuma na Giginya dake Sokoto kana Kontagora a jihar Niger dama na Lafia a jihar Nassarawa da kuma na August 04 dake Damaturu a jihar Yobe.

Ana saran fara wasan farko na gasar tsakanin kungiyar kwallon kafa Junior Kano Pillars da kuma abokiyar hamayyar ta Kwankwasiyya FC wato Samba Kurna.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...