Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniFA Cup:Man City da Man United zasu kece raini da juna a...

FA Cup:Man City da Man United zasu kece raini da juna a wasan karshe

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ,zata fafata da Manchester City a wasan karshe na gasar cin kofin kalubale na kasar Ingila FA Cup.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Man United tayi nasarar doke Brighton da ci 7-6 a bugun daga kai sai mai tsaran gida a ranar Lahadi.

Ita kuwa Man City tin a ranar Asabar ta lallasa Shefield United da ci 3-0 a wasan da suka fafata.

Yanzu haka dai a karon farko a wasan karshe a gasar FA Cup, Man City da Man United zasu kece raini da juna a gasar ta kakar wasannin shekarar 2022/2023.

Kuma ana saran wasan karshen zai gudana a ranar Uku ga watan Yunin bana, kuma babban filin wasan kasar Ingila Wembley ne zai karbi bakuncin wasan.

Latest stories

Related stories