Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniMan City ta koma matakin farko a Teburin gasar Firimiyar Ingila

Man City ta koma matakin farko a Teburin gasar Firimiyar Ingila

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, ta koma matakin farko a gasar Firimiya ta kasar Ingila bayan doke Fulham da ci 2-1.

Nasarar da Manchester City tayi, hakan ya kuma bawa Dan wasa Erling Haaland damar zura kwallo 50 a duka kakar wasanni ta bana.

Haaland ne ya fara zura kwallon farko a bugun daga Kai sai mai tsaran gida a minti na 3, sai kuma dan wasa Carlos Vinicius ya warware kwallon a minti na 16.

Sai dai kuma dan wasa Julian Álvarez ya sanya kwallo ta biyu ga Man City a minti na 36 bayan samun taimakon Riyard Mahrez.

Yanzu haka Dan kasar Norway Halland, ya zamo a gaba-gaba a yawan zura kwallo a gasar Firimiya ta Ingila.

Wanda hakan ke nuna ya kusa kamo Andy Cole da ya zura 34 lokacin ya na Newcastle a kakar 1993-94, kana shima Alan Shearer ya nuna irin bajintar lokacin yana Blackburn a shekarar data biyo baya.

Kawo yanzu Manchester City ta koma saman Arsenal da tazarar maki daya.

Kuma hakan shi ne na farko da Manchester City ta koma saman Arsenal a tsakiyar kakar wasanni, wajen yunkurin lashe gasar Firimiya da Champions League da kuma FA Cup.

Latest stories

Related stories