Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiA karon farko tun shekarar 2020, Messi da Ronaldo zasu kece raini

A karon farko tun shekarar 2020, Messi da Ronaldo zasu kece raini

Date:

A wannan rana gamayyar yan wasan kungiyoyin AL Nassr dana AL Hilal, zasu fafata wasan sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke kasar Faransa.

 

Wasan zai gudana a katafaren filin wasa na King Fahad International da ke kasar Saudi Arabia, karawar da za a kece raini da misalin karfe Tara na dare karkashin jagorancin alkalin wasa Abdulrahman Al-Jassim dan kasar Qatar.

 

Cristiano Ronaldo, a karon farko zai fafata wasa a kungiyar AL Nassar, tun bayan raba gari da tsohowar kungiyarsa ta Manchester United.

 

Rabon da Gwarazan biyu su hadu da juna tun watan Disambar 2020 lokacin da Juventus ta yi nasara a filin wasa na Nou Camp akan kungiyar ta Barcelona da ci 3-0.

 

Kuma ana saran Cristiano Ronaldo zai jagoranci yan wasan da zasu fafata da kungiyar ta PSG a wasan na sada zumunta a wannan rana ta Alhamis.

Latest stories

Related stories