Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar kula da lauyoyi ta bukaci a cire sashe na 65 na...

Majalisar kula da lauyoyi ta bukaci a cire sashe na 65 na sabuwar dokar zabe

Date:

 

Shugaban majalisar kula da lauyoyi ta Nigeria Cif Wole Olanipekun (SAN), ya bukaci majalisar dokokin kasa da ta cire sashe na 65 na dokar zabe, wanda ya bai wa jami’an INEC damar sake duba sakamakon zabe, da nufin yin gyara, bayan an ayyana wanda ya lashe zabe.

 

Olanipekun ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Ado-Ekiti.

 

Ya ce wannan sashe babu shi a cikin tsohuwar dokar zabe ta Nigeria, kuma babu kasar dake da irin wannan tsari a fadin duniya.

 

A cewarsa sashen da yayi wannan bayani yana da hatsarin gaske, kasancewar yau za a iya bayyana wanda ya lashe zabe, gobe kuma a zo a ce bashi bane, wanda hakan zai kawo rudani.

 

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta cire wannan sashe, inda yayi kira ga masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa da su sanya ido sosai kan jami’an hukumar zabe domin kaucewa magudi.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...