Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKano: Kotu ta daure wasu alkalai kan badakalar kudin Marayu

Kano: Kotu ta daure wasu alkalai kan badakalar kudin Marayu

Date:

Wata kotun majistare mai lamba 14, a Jihar Kano ta aike da wasu alkalai da ma’aikatan hukumar shari’a gidan gyaran hali, saboda zargin badakalar Naira miliyan 99.

 

Mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti, ne ya aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wadanda mallakin wasu marayu ne.

 

Tun da fari Hukumar karbar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ce ta gurfanar da alkalai da kuma ma’aikatan hukumar shari’ar Musulunci a gaban kotun.

 

Cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotun sun hada da Sani Ali da Sani Uba Ali da Bashir Baffa da Gazzali Wada da Hadi Tijjani Mu’azu.

 

Sauran sune Alkasim Abdullahi da Yusuf Abdullahi da Mustafah Bala da Jaafar Ahmad da Adamu Balarabe da Aminu Abdulhadi da Abdullahi Sulaiman Zango da Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa da kuma Usaina Imam.

 

Takardar karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira miliyan 99, laifukan da dukkaninsu suka musanta.

 

Sai dai mai gabar da kara, Barista Zaharaddin Kofar Mata, ya roki kotun da ta sake sanya wata ranar domin kara gabatar da wadanda ake zargi tare da kawo shaidu.

 

Tuni dai alkalin kotun ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar daya ga watan Fabrairun 2023.

 

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...