Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMakarantar koyon tukin jirgi sama ta Zariya ta kera jirage 2

Makarantar koyon tukin jirgi sama ta Zariya ta kera jirage 2

Date:

Makarantar koyon tukin jirgin sama da ke Zariya a jihar Kaduna, ta ce nan da watan Mayu zata samar da jirage biyu da ta kera a wannan kasa.

 

Wannan makaranta da aka kafa a shekarar 1964 na horar da masu kera jirgin sama, da masu gyaransa, da wadanda zasu tuka shi, da dai sauran bangarorin sufurin jiragen sama.

 

Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka a taron majalisar zartarwa ta tarayya.

 

Ya ce majalisar ta amince da kashe kudi fiye da naira milyan dubu biyu wajen kera jirgin sama na Magnus Centennial a makarantar ta Zariya.

 

Ya kuma tabbatar da cewa, ana sa ran samun wannan jirgi har guda biyu kafin karewar wa’adin gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Mayun bana.

 

Hadi Sirika ya ce nan ba da jimawa ba, Nijeriya za ta fara kera jiragen sama da hadin gwIwar kamfanin kera jiragen sama na kasar Hungary da zai bude reshensa a Zariya.

Latest stories

Related stories