Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKudirin gyaran dokar fansho ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano

Kudirin gyaran dokar fansho ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Kudirin gyaran dokar harkokin fansho, dana dokar baiwa mata masu ciki da yara kanana kulawa kyauta a asibitoci sun tsallake karatu na farko a gaban majalisar dokokin Kano.

 

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano

Majalisar karkashin kakakinta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ta amince da karatun farko na kudurorin a zamanta na larabar nan.

Sauran kudurorin da suka tsallake karatun farko sun hada da gyaran dokar hadaka ta karbar haraji tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi da gyaran dokar rage mambobin majalisar sarakuna da kuma dokar hukumar majalisar dokokin Kano.

Haka zalika kudirin gyaran dokar sufuri ta shekarar 1963 ya tsallake karatun farko a zaman majalisar.

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano

Yayin zaman dai majalisar tayi karatun farko kan rahoton kasafin kudin badi da ya zarta naira miliyan dubu dari biyu da arba’in.

 

Majalisar dokokin ta Kano ta kuma dage zamanta zuwa gobe alhamis.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...