Premier Radio 102.7 FM
Kiwon Lafiya Labarai

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano

A dai zaman majalisar dokokin Kano na Larabar nan majalisar ta bada umarnin dakatar da gina shaguna da ake yin kurin yi a kofar shiga asibitin “IDH” da ake kira asibitin (Zana).

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Tukur Muhammad Fagge, ne ya gabatar da kudirin gaggawa inda kuma ya samu amincewar majalisar.

Tukur Muhammad Fagge, ya ce gina shaguna a kofar asibitin zai kawo barazana ga marasa lafiya dake zuwa asibitin.

Muna kashe miliyan 30 don siyan man diesel– Asibitin Aminu Kano

Majalisar ta kuma kafa kwamitin bincike kan batun gina shagunan karkashin kwamitin lafiya da kasa da kuma Muhalli na majalisar inda ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotansa a ranar Talata mai zuwa 21 ga watan da muke ciki.

Wakilin mu na majalisa Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa majalisar ta dage zamanta zuwa ranar Litinin 20 ga watan Yunin da muke ciki.

A Wani Labarin...

Muhimman abubuwa 5 da zan mayar da hankali in na zama shugaban kasa: Atiku Abubakar

Mukhtar Yahya Usman

Damfara:Kotu ta bada umarnin sake gurfanar da A A Zaura

Mukhtar Yahya Usman

Yanzu-yanzu: PDP ta bukaci a rushe shugabacinta a Kano

Mukhtar Yahya Usman