Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciZa'a fara amfani da kudin bai daya na (ECO) a kasashen afurka.

Za’a fara amfani da kudin bai daya na (ECO) a kasashen afurka.

Date:

Shugaban kungiyar kasashen yammacin afurka (ECOWAS) Mr, Jean-Claude Brou, ya bayyana cewa kungiya ta cigaba da zama don kaddamar da kudin bai daya na kasashen mai suna “ECO” a shekarar 2027.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Mr, Jean-Claude Brou, ya bayyana hakane a Talatar nan yayin da yake gabatar da rahoto ga majalissar kungiyar a zaman farko na shekarar 2022 da kungiyar ta saba gabatarwa a Abuja.

Asibitin Aminu Kano ya kara kudin ganin likita da kudin wasu aikace aikace a asibitin.
Ya ce an dakatar da shirin kaddamar da kudin ne sakamakon bullar annobar korono daga shekarar 2020 wanda hakan ya tilastawa kasashen maida hankali wajen shawo kan cutar.

Ya ce dole ne ayi zaman ta yadda da zarar an kaddamar da kudin zai ishi ‘yan kasa gaba daya.

“Dole ne mu dakatar da shirin a shekarar 2022, da 2021 kuma muna kallon shekarar 2022 da 2026 don samar da ka’idoji da zasu bamu damar yin shiri kan tattalin arziki,” a cewar sa.

Idan za’a iya tunawa dai a shekarar 2019 ne shugabanin kasashen afurka na kungiyar ECOWAS suka amince da samar da kudin bai dayan tare da sanya masa suna “ECO” yayin wani zama da sukayi a birnin tarayya Abuja.

Latest stories

Related stories