Premier Radio 102.7 FM
Labarai Tsaro

Sojoji sun sake ceto daya daga cikin ‘yan matan Chikbok

Rundunar sojin kasar nan ta ceto daya daga cikin ‘yan matan Chikbok.

Rundunar sojin kasar nan a Talatar nan ta gano wata mai suna Mary Ngoshe, daya daga cikin ‘yan matan makarantar sakandire ta Chibok da Boko Haram suka a shekarar 2014.

Rundunar ta gano tane rike da jariri wanda ake zargin nata ne yayin da suke sunturi a yankin Ngoshe na jihar Borno.

Wannan na kunshene cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar nan ta fitar a shafinta na Twitter a safiyar Laraba.

“Rundunar soji ta 26 yayin sunturi a yankin Ngoshe a jihar Borno ta gano wata mai suna Mary Ngoshe wacce daya ce daga cikin ‘yan matan makarantar sakandire ta Chibok ta aka sace a shekarar 2014”, a wallafar Twitter ta rundunar.

A Wani Labarin...

Karamar hukumar Dawakin Tofa ta haramta zancen dare

Mukhtar Yahya Usman

Barau ya fasa takarar gwamna, ya sayi fom din sanata

Mukhtar Yahya Usman

Babban taron APC zai ɗinke ɓarakar da ke cikin jam’iya — Ganduje

Aminu Abdullahi Ibrahim