Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalissar dokokin Kano: Matemakin shugaban masu rinjaye ya ajiye mukaminsa

Majalissar dokokin Kano: Matemakin shugaban masu rinjaye ya ajiye mukaminsa

Date:

Matemakin shugaban masu rinjaye na majalissar dokoki ta jihar Kano kuma dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, ya ajiye mukaminsa na matemakin shugaban masu rinjaye.

Ya mika takardar ajiye mukamin nasane a Talatar nan yayin zaman majalissar inda shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta.

‘Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP
Tuni dai ‘yan majalisar suka zabi dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Rogo, Magaji Dahiru Zarewa, a matsayin sabon matemakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin.

Haka zalika majalisar ta karbi takarda daga ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano dake neman a tantance Umar Isah Sarki, a matsayin sakataren gudanarwa na karamar hukumar Rano biyo bayan ajiye aiki da tsohon sakataren gudanarwar karamar hukumar Jamilu Hassan.

Majalisaar ta mikawa kwamitin kananan hukumomi na majalissar takardar don yin nazari akai.

A wani cigaban kuma majalisar zartaswa ta jihar Kano ta aikewa da majalissar dokokin bukatar yin doka kan maida asibitin Muhammad Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nasarawa zuwa asibitin koyarwa.

Haka zalika gwamnatin Kano ta bukaci majalisar tayi nazari kan dokar karawa malaman makaranta wa’adin yin ritaya na shekarar 2022.

Majalisar ta kuma karbi takarda dake bukatar tantancewa da tabbatar da Malam Isma’il Musa a matsayin babban mai binciken kudi na jihar Kano inda majalisar ta aike da takardar ga kwamitinta kan sha’anin kudi domin nazari akai.

Majalissar ta kuma sake dage zamanta zuwa gobe Laraba goma sha biyar ga watan da muke ciki bayan da shugaban masu rinjaye Abdul Madari mai wakiltar karamar hukumar Warawa ya gabatar da bukatar dage zaman inda ya samu goyan bayan dan majalisa mai wakiltar Gezawa Isyaku Ali Danja.

Latest stories

Related stories