Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta gindayawa kamfanonin sada zumunta sharuda

Gwamnatin tarayya ta gindayawa kamfanonin sada zumunta sharuda

Date:

Gwamnatin tarayyya ta fitar da wasu dokoki ga kamfanonin shafukan sa da zumunta na Tuwita da Facebook da WhatsApp da Instagram da Google da TikTok da sauransu kan ayyukansu a ƙasar nan.

Hukumar ci gaban Fasahar Sadarwa ta Najeriya NITDA ce ta fitar da sababbin sharuɗɗan, sakamakon umarnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Dokokin, waɗanda aka samar da su don sa ido a kan yadda shafukan sa da zumuntar ke aiki, sun bayyana cewa dole kowane kamfani da ke aiki a Najeriya ya samar da duk bayanansa.

Sannan dole ya taimaka wa duk wata hukuma ta gwamnati da abin da take buƙata da nufin aiwatar da bincike ko shawo matsalolin laifukan intanet ko kuma shigar da ƙara a kan laifi.

Gwamnatin tana kuma so shafukan sa da zumuntar su kiyaye dokokin Najeriya kuma kar su yi duk wani abu ko wata kwaskwarima da za su yi katsalandan ga dokokin ƙasar nan.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...