Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnonin G5 na PDP sun sake ganawa a London.

Gwamnonin G5 na PDP sun sake ganawa a London.

Date:

Gwamnoni biyar na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Nyesom Wike na jihar Rivers, sun yi taro a birnin London, a ci gaba da tattaunawarsu don samar da matsaya gabanin zaben 2023.

Kungiyar da ta hada da gwamna Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo, Ifeanyi Uguanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abia, sun bar Najeriya ne jiya Litinin, domin yin taron.

Kungiyar gwamnonin dai ta dage kan kiran da suka yi na a tsige shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu tare da zabar wani daga yankin Kudu a matsayin shugaban jam’iyyar.

Don haka kungiyar ta janye goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, bisa zarginsa da kin amincewa da bukatarsu.

Latest stories

Related stories