Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniPortugal na shirin karbar bakuncin Najeriya a wasan sada zumunci

Portugal na shirin karbar bakuncin Najeriya a wasan sada zumunci

Date:

A wannan rana ta Alhamis 17 ga Nuwambar 2022, Najeriya ke shirin buga wasa da kasar Portugal a wasan sada zumunci, gabannin fara gasar cin kofin duniya a Qatar.

 

Wasan dai zai gudana a Alhamis dinnan a filin Jose Alvalade da ke birnin Lisbon na kasar ta Portugal da misalin 7:45 agogon Najeriya.

 

Kasar Portugal wadda na cikin kasashe 32 da zasu halarci kofin duniya na wannan shekara, za tai amfani da wasan ne domin kara shiri.

 

Ita kuwa Najeriya zata buga wasan ne domin shirin buga wasan share fage na buga gasar cin kofin Nahiyar Afrika a shekara Mai zuwa.

 

Portugal karkashin jagorancin Mai horar da ita Fernando Santos tuni ake saran ka iya fani da ‘Yan wasa kamar haka….

 

Portugal predicted XI: Sa; Dalot, Silva, Pereira, Guerreiro; Palhinha, Neves, Vitinha; Leao, Otavio, Ramos.

 

Najeriya kuwa karkashin jagorancin Jose Peseiro ka iya amfani da Yan wasa kamar haka….

 

Nigeria predicted XI: Uzoho; Awaziem, Troost-Ekong, Bassey, Akpoguma; Onyeka, Ndidi, Iwobi; Chukwueze, Dennis, Onuachu.

 

To Amma Dan wasan Cristiano Ronaldo, ba lallai ya buga wasan ba sabida ciwon ciki da ya ke fama da shi.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...