Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Saturday, April 13, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniOsimhen ya zura kwallo ta Tara a Napoli a gasar Serie A

Osimhen ya zura kwallo ta Tara a Napoli a gasar Serie A

Date:

Dan wasan gaba na Najeriya da kungiyar kwallon kafa ta Napoli Victor Osimhen ya zura kwallo ta tara a wasan da Napoli ta doke Udinese da ci 3-2 a ranar Asabar.

 

Kungiyar kawo yanzu ta bayar da ta zarar maki 11 a gasar ta Serie A bayan buga wasa 15 da Napoli tayi.

 

Napoli karkashin jagoranci Luciano Spalletti’s ta samu nasarar wasanne bayan da ‘Yan wasa irinsu Osimhen, Piotr Zielinski da Eljif Elmas suka zura kwallaye ukun.

 

Wasan wanda ya gudana kuma ya samu halartar magoya baya akalla 50,000 a filin na Stadio Maradona.

 

Yanzu haka Napoli itace a mataki na farko a gasar ta Serie A a kakar wasannin shekarar 2022/2023.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...