Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniBabu sunan Ahmad Musa cikin wanda zasu buga wasan Najeriya da Portugal

Babu sunan Ahmad Musa cikin wanda zasu buga wasan Najeriya da Portugal

Date:

Mai horar da tawagar Super Eagles  Jose Peseiro, ya cire sunan Kyaftin Najeriya Ahmad Musa da Dan Wasan Queens Park Rangers’ Leon Balogun, daga jerin wanda zasu buga wasan sada zumunci da kasar nan zatai da Portugal.

 

 

Wasan dai zai gudana a birnin Lisbon a ranar Alhamis mai zuwa tsakanin kasashen biyu.

 

 

Sai dai cikin jerin ‘Yan wasa 23 da Peseiro ya gayyata akwai mataimakin Kyaftin din tawagar William Troost-Ekong, da Mai tsaran raga Francis Uzoho da kuma Wilfred Ndidi.

 

 

Ana saran fafatawar tsakanin kasashen biyu zata gudana a filin wasa na Estadio Jose Alvalade da ke birnin na Lisbon da misalin karfe 7.45 agogon Najeriya.

 

 

Kasar Portugal dai na shirin buga gasar cin kofin duniya a Qatar, wanda zatai amfani da wasan na sada zumunci da Najeriya domin shirin tunkarar gasar.

 

 

A gefe guda kuwa Super Eagles bata cikin jerin wanda zasu wakilci Nahiyar Afrika a gasar ta cin kofin duniya.

 

 

Bayan da a wasan share fage kasar Ghana ta doke Najeriya a wasa gida da waje da suka fafata.

 

 

Kawo yanzu cikin Jerin ‘Yan wasa 23 da zasu buga wasan, sun hada da masu tsaran raga kamar Maduka Okoye (Watford FC, England); Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Adebayo Adeleye (Hapoel Jerusalem, Israel)

 

 

Daga bangaren ‘Yan wasan baya kuwa sun hada da William Ekong (Watford FC, England); Olisa Ndah (Orlando Pirates, South Africa); Calvin Bassey (Ajax FC, The Netherlands); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany); Chidiebube Duru (Rivers United); Tyronne Ebuehi (Empoli FC, Italy); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal); Bright Osayi Samuel (Fenerbahce FC, Turkey)

 

 

Sai Kuma’Yan wasan tsakiya akwai Joseph Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Alex Iwobi (Everton FC, England); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Oghenekaro Etebo (Aris Thessaloniki, Greece)

 

 

‘Yan wasan gaba kuwa akwai Moses Simon (Nantes FC, France); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Terem Moffi (Lorient FC, France); Paul Onuachu (Genk FC, Belgium); Victor Osimhen (SSC Napoli, Italy); Emmanuel Dennis (Nottingham Forest, England)

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...