Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniTennis: Carlos Alcaraz ya lashe gasar US Open a karon farko

Tennis: Carlos Alcaraz ya lashe gasar US Open a karon farko

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

 

Matashin dan wasan kasar Spain, Carlos Alcaraz burinsa ya ciki bayan lashe gasar US Open a karon farko a tarihi.

 

Carlos Alcaraz ya yi nasara a zagaye hudun da suka fafata a kan dan wasa Casper Ruud da ci 6-4 da 2-6 fa 7-6 da kuma 6-3.

 

Mai shekara 19 shi ne matashi wanda ya nuna bajinta ta lashe Grand Slam, tin bayan da Rafael Nadal ya lashe gasar French Open a shekarar 2005.

 

Yanzu haka dai dan wasa Carlos Alcaraz shi ne na farko a jerin matasa a fagen tennis, sai kuma Casper Ruud wanda kuma shi ne na biyu a fagen Tennis a duniya bangaren matasa maza masu kanan shekara.

 

Gasar US Open dai ta gudana a birnin New York na kasar Amurka, wadda aka fara tin daga shekarar 1987.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...