27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiWasanniBayern Munich ta lallasa Barcelona a gasar Champions League

Bayern Munich ta lallasa Barcelona a gasar Champions League

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, ta casa Barcelona da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun turai a ranar Talata.

 

Wasan da ya gudana a filin Allianz Arena da ke birnin Munich na kasar Jamus karkashin jagorancin alkalin wasa Danny Makkelie.

 

Dan wasa Lucas Hernandez ne ya fara zura kwallon farko a minti na 50, bayan samun taimako daga Joshua Kimmich.

 

Sai dai aminti na 54 dan wasa Leroy Sane ya Kara kwallo ta biyu ma kungiyarsa ta Bayern Munich.

 

Wasan dai shi ne na biyu a rukunin C wanda Bayern Munich ta ke a matakin farko da maki 6 bayan buga wasa biyu.

 

Ita kuwa Barcelona na mataki na biyu da maki uku, kuma zata ziyarci Inter Milan a wasa na gaba a ranar hudu ga watan Oktoba mai kamawa.

 

Sauran wasannin da suka gudana a ranar Talata 13 ga Agustan sun hada da…….

 

Victoria PLZen 0 Inter Milan 2

 

Sporting 2 Tottenham 0

Liverpool 2 Ajax 1

 

FC Porto 0 Club Brugge 4

 

Bayern Leverkusen 2 Atletico 0

 

Marseille 0 Frankfurt 2

Latest stories