Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWanda ake saran ka iya maye gurbin Thomas Tuchel da Chelsea ta...

Wanda ake saran ka iya maye gurbin Thomas Tuchel da Chelsea ta sallama

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale

 

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sanar da sallamar Thomas Tuchel a matsayin mai horarwa a wannan rana ta 7 ga Satumbar 2022 karkashin jagorancin mamallakinta Todd Boehly .

 

Sai tuni tuni ake saran guda cikin masu horarwa hudu da ya ka iya zama sabon mai horar da kungiyar ta Chelsea da ke London a Ingila.

 

Thomas Tuchel ya kama aiki da kungiyar a watan Janirun 2021, wanda ya lashewa Chelsea Champions League, UEFA Super Cup da kuma Club World Cup.

 

To amma mene dalilin sallamar Thomas Tuchel ?

 

A wasan farko na gasar cin kofin zakarun turai Chelsea tayi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Dinamo Zagreb wasan da ya gudana a ranar Talata.

 

Haka kuma shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Todd Boehly ya ware fam miliyan 280 ga tawagar domin siyan sabbin ‘yan wasa, amma har kawo yanzu al’amura sun gaza ta fiya yadda ya kamata.

 

To ammma wannnan ba sabon abu a bane a tarihin kungiyar, domin kuwa ko a baya karkashin tsohon mamallakin kungiyar Roman Abramovich Chelsea bata jira da zarar mai horarwa ya fara gaza abin azo a gani.

 

Da ake kallon tarihi ne ya maimaita kansa Kamar yadda yake a baya ga wanda ke bibiyar yadda ake tafiyar da kungiyar tun lokacin Roman Abramovich ba zai yi mamaki ba da daukar irin wannan mataki ba.

 

Hakan na nufin kungiyar ta Stamford Bridge ta yi abinda ta saba, wato rashin yiwa mai horarwa uzuri ko da ya yi abun azo a gani a baya, wanda hakan ya sa ta salami wanda yam aye gurbin Frank Lampard.

 

Ko a baya idan aka duba tarihi, Chelsea ta salami Jose Mourinho bayan ya lashe Firimiya, kuma haka ta yiwa Antonio Conte, ba yaga Di Matteo da lokacinsa har kofin zakarun turai ya dauka, da kuma kofin kalubale wanda shi mai horarwa ne na riko.

 

Cikin nasarorin Thomas Tuchel da yayi a Chelsea sune Jagorantar kungiyar wasanni 100, inda yayi nasara a 60, rashin nasara a 16 da kuma kunnan doki a wasa 24.

 

Kuma ya lashe Champions League da UEFA Super Cup da FIFA Club World Cup.

 

Amma ya kai kungiyar wasan karshe a gasar kofin kalu bale na FA Cup sau biyu, da kuma kofin League Cup amma bai yi nasara ba.

 

Ga jerin wanda a ciki a ke saran zai maye gurbin Thomas Tuchel a Chelsea.

 

1- Mauricio Pochettino

 

Dan kasar Argentina, kuma tsohon mai horar da Paris Saint-Germain da Tottenham Mauricio Pochettino.

 

2- Graham Potter

 

Wanda a yanzu haka shi ne mai horar da kungiyar da ke buga gasar Firimiya ta Ingila wato Brighton wato Graham Potter.

 

3- Zinedine Zidane

 

Zinedine Zidane wana da kansa ya ajjiye aikin horar da Real Madrid, bisa yadda har kawo yanzu ba shida kungiyar da yake horarwa.

 

A tarihi ya lashe gasar Champions League har sau uku a jere, kuma ake kallon Todd Boehly ka iya zaba don aikin horar da Chelsae.

 

4-Marcelo Bielsa

 

Wanda ya taba jagorantar Leeds United, kuma ya taka rawar gani matuka a lokacin da ya kasance da kungiyar da ke buga gasar Firimiyar Ingila.

 

5- Diego Simeone

 

Diego Simeone, shi ne mai horar da Atletico Madrid wanda ya bawa kungiyar gudunmawa wajen lashe gasar La Liga a baya, kuma kai kungiyar wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai har sau biyu, amma ba suyi nasara ba.

 

6- John Terry

 

John Terry wanda tsohon dan wasan Chelsea ne, kuma ya taka rawar gani sosai, lokacin da ya bugawa kungiyar da ke London wasa.

 

A baya kuma, ya kasance a kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa karkashin jagorancin Dean Smith.

 

Kawo yanzu wanda kungiyar zata dauka shi ne abin jira, wanda kuma zai fuskanci sabon kalu bale a kungiyar da ta sayi sabbin ‘yan wasa irinsu………..

 

Raheem Sterling daga Manchester City a kan kudi fam miliyan 50.

 

Kalidou Koulibaly daga Napoli a kan kudi fam miliyan 34.

 

Sai Omari Hutchinson daga Arsenal, akwai Gabriel Slonina daga Chicago Fire a kan kudi fam miliyan 12.

 

Carney Chukwuemeka daga Aston Villa kan fam miliyan 20 da Marc Cucurella daga Brighton da Hove Albion kan kudi 55.

 

Sai Wesley Fofana a kan kudi 72 daga Leicester City, har mada Pierre-Emerick Aubameyang daga Barcelona a kan kudi 10, sai kuma Denis Zakaria daga Juventus a matsayin aro.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...