33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiWasanniWasannin farko na rukuni a gasar Champions League na 2022/2023

Wasannin farko na rukuni a gasar Champions League na 2022/2023

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Daga Ahmad Hamisu Gwale

 

A wannan rana ta Talata, shida ga Satumbar shekarar da muke ciki, za a fara gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta kakar wasannin shekarar 2022/2023.

 

Gasar wadda Kungiyoyi 32 zasu fafata daga sassa daban-daban na kasashen nahiyar turai, da ake saran Fara wasannin rukuni daga shida ga Satumba, zuwa biyu ga Nuwambar da muke ciki kwanaki kadan kafin fara gasar cin kofin duniya a Qatar.

 

Yayinda kuma wasannin kwaf daya zasu gudana a ranar 14 ga Fabrairun shekara mai zuwa, inda kuma a buga a wasan karshe na gasar a ranar 10 ga Yunin 2023 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

 

Wasan farko na matakin rukuni zasu fara daga a wannan rana ta shida ga watan na Satumba sun hada………

 

Dinamo Zagreb da Chelsea da karfe (18:45)

 

Borrussia Dortmund da Copenhagen da karfe (18:45)

 

Salzburg da AC Milan da karfe (21:00)

 

Celtic da Real Madrid da karfe (21:00)

 

Leipzig da Shakhtar (21:00)

 

Sevilla da Man City (21:00)

 

Paris da Juventus (21:00)

 

Benfica da Maccabi Haifa(21:00)

 

A kakar wasannin da ta gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce ta lashe gasar, bayan doke Liverpool da ci 1-0 a wasan karshen da suka fafata

Latest stories