Daga Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kawo karshen nasarar Arsenal na wasa biyar a gasar Firimiyar Ingila.
Arsenal tayi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 3 da 1 a ranar Lahadi 04 ga Agustan 2022 a filin wasa na Old Trafford.
Sabon dan wasan da Manchester United ta siya Antony ne ya fara zura kwallon farko a minti na 34 kafin aje hutun rabin lokaci.
Sai dai dan wasa Bokayo Saka ya warware kwallon a minti na 59, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Amma dan wasan kasar Ingila Marcos Rashford ya tabbatar da nasarar Manchester United, bayan zura kwallaye biyu a minti na 65 da 74.
Wanda hakan ya kawo karshen nasarar Arsenal na yin nasara a wasanni biyar a gasar Firimiya ta Ingila.
Sai dai har kawo yanzu Arsenal itace a matakin farko a gasar Firimiya da maki 15, bayan nasara a duka wasanni biyar da tayi.
Yayinda Manchester United ke mataki na biyar da maki 12 a wasanni shidan da ta yi a sabuwar kakar wasannin shekarar 2022/2023.
A wasan mako na bakwai a ranar 11 ga watan da muke ciki, Arsenal zata karbi bakuncin Everton.
Ita kuwa Manchester United zata ziyarci Crystal Palace a wasan na mako na bakwai na gasar Firimiya ta kasar Ingila.