Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoZamu shigar da sabuwar kara a kotun koli cewar Gwamnan Kano Injiniya...

Zamu shigar da sabuwar kara a kotun koli cewar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

Date:

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce zasu shigar da sabuwar ƙara a kotun koli ta Najeriya kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi.

Gwamnan ya ce suna ganin kotun ɗaukaka ƙara bata yi musu adalci ba, amma suna da kyakykyawan fatan kotun koli zata yi musu adalci.

Ya kara da cewa tuni suka umarci lauyoyinsu su shigar da sabuwar kara don kalubalantar hukuncin baya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace wannan matsalar da ta faru ta takaitaccen lokaci ce, kuma yana da yakinin kotun ƙoli zata kwatowa alummar Kano hakkinsu.

A ranar juma’a ne kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a Kano, Inda ta ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC shine halastaccen wanda ya lashe zaben gwamna a Kano na 2023.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...