Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMagoya bayan jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun fara bayyana irin...

Magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun fara bayyana irin fatan da suke da shi kan hukuncin shari’ar zaben gwamna

Date:

Magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun fara bayyana irin fatan da suke da shi kan hukuncin shari’ar zaben gwamna da kotun daukaka kara zatayi a juma’ar nan
Wannan ya biyo bayan sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafins a na Facebook da ke cewa sun samu bayani daga tawagar lauyoyinsu cewar kotun zata yanke hukuncin a safiyar juma’ar nan.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf ne dai ya daukaka kara inda ya kalubanci hukuncin kotun kararrakin zabe da ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen wanda Kanawa suka zaba.

Umar Haruna Makoda, dan jamiyyar NNPP ne, yace suna da tabbacin kotun daukaka karar zata yi musu adalci

Ibrahim Aminu Ibrahim dan jam’iyyar APC shima yace suna da kwarin gwuiwa zasu samu nasara kamar yadda kotun farko ta yi hukunci a baya.

Ra’ayoyi yayan jamiyyar NNPP da APC kenan da kowannensu ke fatan nasara a gobe juma’a da kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano.

Latest stories

Related stories