Yayin da ake dakon hukucin kotun daukaka kara a safiyar yau juma’a, dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, da kotun sauraron korafin zabe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano ya ce yana kyautata zaton shi ne zaiyi nasara
Gawuna yace a halin yanzu, zaton da alúmmar jihar Kano suke yi masa na kawo cigaba mai dorewa kuma tabbatacce, yafi bashi tsoro a kan shari’ar ma gaba dayanta da kuma hukuncin da za’a yanke.
