Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama wadanda ke kai hare-hare...

Mun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama wadanda ke kai hare-hare da satar mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

Date:

Rundunar sojin saman kasar nan ta samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama wadanda ke kai hare-hare da satar mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, da ma yankin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar ta Kaduna.

Kakakin rundunar sojojin saman, Air Comodore Edward Gabkwet, ya shaidawa manema labarai cewa an kaddamar da farmakin ne domin kakkabe ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

Ya kuma tabbatar da cewa dan fashin dajin nan Bodari na cikin wadanda aka kai wa farmaki, sai dai bai iya tabbatar da ko an kashe shi ba.

A wani labarin kuma hukumomi a jihar Neja sun ce wasu jami’an tsaron sa kai da jami’an tsaron kasar sun samu nasarar ceto sama da mutane ashirin, tare da hallaka ‘yan bindiga da dama a jihar.

Shugaban karamar hukumar Muye, Najume Kuci, ya ce sun shafe tsawon shekara biyar su na fama da matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankinsu, kuma sabboda kamari da matsalar ta yi ya sa suka tunkari gwamnatin jihar.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...