Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIna zargi APC da kokarin amfani da kotuna wajen mayar da kasar...

Ina zargi APC da kokarin amfani da kotuna wajen mayar da kasar nan kan tsarin jam’iyya daya – Atiku Abubakar

Date:

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi jam’iyyar APC da kokarin amfani da kotuna wajen mayar da kasar nan kan tsarin jam’iyya daya.

Alhaji Atiku Abubakar da yayi takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Maris na bana na martani ne dangane da korar wasu gwamnonin kasar nan daga kujerunsu da hukuncin kotun daukaka kara ya zartar, ciki har da na nan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da na Zamfara, Dauda Lawal, da na Filato, Caleb Muftwang.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce an san dimokuradiyya da tabbatar da ‘yancin jama’a wajen zabar wanda suke so, da ma ba ‘yan adawa damar bayyana ra’ayinsu.

Da yake karin bayani ga Premier Radio, hadimin Atiku Abubakar kan kafofin labarai, Abdul-Rashid Shehu, ya ce akwai fargabar shugaba Bola Tinubu zai mayar da kasar nan kamar lokacin da ya mulki jihar Lagos, wato ba tare da jami’iyyar hamayya na samun ta cewa ba…

Jam’iyyar PDP dai na ganin mayar da bangaren shari’a dandalin mika cin hanci da rashawa da musgunawa ‘yan adawa matakan tauye dimokuradiyya ne da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya dauka.

Latest stories

Related stories