Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSiyasaZaben 2023: Hare haren yan bindiga na maida hannun agogo baya a...

Zaben 2023: Hare haren yan bindiga na maida hannun agogo baya a Najeriya | Premier Radio | 13-01-2023

Date:

Ubaida Muhammad Lawan

 

Gabanin babban zaben badi, hare-hare na ta kara kamari a ofisoshin zabe da kuma hallaka jami’an tsaro daban daban a Najeriya, duk da irin alwashin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke ikirin yi ga matsalar tsaron da kuma tabbatar da an gudanar da babban zaben cikin lumana.

Hare haren dai a iya cewa kullum jiya i yau, abinda ya kai ga al’umma da dama ke shakkun yuwuwar zaben badi kamar yadda aka tsara, amman Shugaban hukumar zaben na kasa yace ba gudu ba ja da baya.

Kididdigar da Hukumar zaben ta kasa INEC ta fitar ya bayyana cewar an kai hari sau 50 a ofisoshin zabe daban daban dake fadin kasar nan daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2022.

Ta ce hare haren sun faru ne a jahohi 15 da suka hada da jihar Imo, Osun, Enugu, Akwa Ibom, Ebonyi, Cross River da kuma Abia.

Sauran sune Anambra, Taraba, Kaduna, Borno, Bayelsa, Ondo, Lagos da kuma jihar Ogun.

2020 ce shekarar da aka fi samun hare hare, inda suka kai akalla sau 22, sai kuma 2021 mai hare hare 12 da kuma shekarar 2019 da shekarar 2022 da aka samu hare hare sau takwas takwas a cewar hukumar zaben.

INEC ta kara bayyana cewar hare haren sun fi kamari a jihohin kudu maso gabas, inda kabilar igbo suka fi rinjaje, wadanda hukumomi suke zargin mayakan ESN na kungiyar Ipob da ke neman kafa kasar Biafara, inda har hukumar zaben ke da niyyar sauyawa wasu daga cikin ofisoshinta mazauni a wuraran da ke fama da wadannan hare haren.

Dacta yahuza Getso, masani ne dangane da harkokkin tsaro da bincike da ta’ammali da bayanan sirri a kasashen Africa, ya bayyana takaicinsa game da wadannan hare hare da suke faruwa a sassan kasar.

Ya ce gwamnati kamata yayi ta kara ingantattun jami’an tsaro wadanda suke da gogewa a harkar tsaro, mafarauta da kuma zaratan matasa tare da basu horo na musamman don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

A ranar 25 ga watan Fabarairun 2023 aka tsara fara kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen da ‘yan kasar  za su zaɓi shugaban ƙasa, gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Rundunar Yan sanda zata tabbatar da tsaro yayin ziyarar Remi Tinubu Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kara nanata cewa...