Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTsaro: Yan bindiga sun kai hari a tashar jirgin Kasa da ke...

Tsaro: Yan bindiga sun kai hari a tashar jirgin Kasa da ke jihar Edo

Date:

Wasu Yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kai hari tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo tare da garkuwa da fasinjoji masu tarin yawa a maraicin ranar Asabar.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin kasa zuwa garin Warri da ke jihar Delta.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kawo yanzu ba a samu labarin rasa rai ba.

 

Sai dai ya ce wasu fasinjojin sun samu raunukan, biyo bayan harbin bindiga daga maharan.

 

Wannan dai na zuwa ne kasa da shekara guda bayan da ‘yan ta’adda da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wanda yayi sanadin garkuwa da fasinjoji masu yawa.

 

Lamarin da ya janwo suka kwashe tsowon watanni a hannun ‘yan bindigar, kafin daga bisani wasu daga cikinsu su shaki iskar yanci.

Latest stories

Related stories