Karibullah Abdulhamid Namdobi
Sabuwar dakar babban bankin kasa CBN ya sanya ta takaice cire kudi a kasar nan ta fara aiki yau litinin 9 ga watan janairun 2023.
CBN dai ya sanya dokar takaita cire kudi a rana guda, inda mutum daya ke da damar cire naira dubu 500 yayin da kamfanoni suke da damar cire miliyan 5.
Baya ga haka bankin na CBN ya umarci bankuna a kasar nan su daina sanya tsaffin kudi a na’urar ATM.
Umarnin dai na zuwane yayin da a karshen watan Janairu za a daina amfani da tsaffin kudi na naira 1000 da 500 da 200 a fadin Najeriya.
Sabbin dokokin da CBN ya sanya wasu na ganin zasu taimaka wurin takaita zagayawar kudi barkatai tsakanin alumma a kasar nan.
A gefe guda kuma dokokin sun janyo cece-kuce, abinda har yanzu wasu ke kokawa kan irin yadda lamarin ka iya janyowa wasu yan kasar nan asara.