Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYakamata mata su maida hankali kan sana’ar wanzanci –Sarkin Wanzamai.

Yakamata mata su maida hankali kan sana’ar wanzanci –Sarkin Wanzamai.

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Masarautar wanzamai ta jihar Kano ta bukaci ‘ya’yan wanzamai mata da su mayar da hankali wurin gadon sana’ar wanzanci domin taimakawa yan uwansu mata.

 

Sarkin wanzaman Kano Alh. Na Bango ne yayi wannan kiran, ya yin bitar kwanaki bakwai da masarautar wanzaman ta shiryawa ‘ya’yan wanzamai mata kan yadda za su nakalci sana’ar.

 

Alh Na Bango ya ce sun shirya bayar da horon ne don ganin cewa ya yansu mata wanzamai sun koyi sana’ar domin taimakawa mata, mai makon maza su dinga duba su.

 

Yayin bitar dai an koyawa matan yadda za su yi sana’ar wanzanci, ta hanyar unguwar zoma, kaho, aski, kaciya, da dai sauran sana’ar wanzanci.

 

Wadanda suka sumu horon sun yabawa masarautar wanzaman ta jihar Kano bisa wannna horo da suka samu.

Latest stories

Related stories