Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda gobara tayi barna a babbar kasuwar Patiskum a jihar Yobe

Yadda gobara tayi barna a babbar kasuwar Patiskum a jihar Yobe

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Wata gobara da ta tashi tayi sanadin kone babbar kasuwar Patiskum da ke jihar Yobe.

 

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da karfe 8 na daren ranar Lahadi

 

Gobarar ta kuma lalata dukiya mai tarin yawa, bayan da ta shafi sassan da ake hada-hadar kayan gwanjo da wurin masu sayar da doya da sauran sassa na kasuwar.

 

Kawo yanzu babu wani rahoto da ya nuna an samu asarar rayukan jama’a a yayin gobarar, sai dai an tafka asarar dukiya mai yawan gaske.

 

Wadanda lamarin ya faru kan idonsu sunce gobarar ta tashi daga bangaren masu sayar da gwanjo. Kawo lokacin hada wannan rahoto babu bayanin musabbabin tashin gobarar.

 

 

Karo na 2 kenan cikin shekaru 2 ana samun tashin gobara a kasuwar ta Patiskum dake jihar Yobe.

 

Latest stories

Related stories