Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMasu adawa da ni zasu yi nadama-Kwankwaso | Premier Radio | 13-01-2023

Masu adawa da ni zasu yi nadama-Kwankwaso | Premier Radio | 13-01-2023

Date:

Abdurrashid Hussain

 

Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace duk wani dan siyasar Kano da yayi adawa dashi a zaben 2023 dake tafe, zaiyi da na sanin yin hakan.

 

Kwankwaso na wannan batu ne bayan da aka jiyo gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na cewa, al’ummar Kano zasu maimaita abinda ya faru a shekarar 1993, inda suka ki zabar dan asalin jihar suka zabi MKO Abiola.

 

Ganduje yace zasu zabi dan takarar su na jamiyyar APC Bola Ahmerd Tinubu da tarin kuri’u a jihar Kano maimakon Kwankwaso dake a matsayin dan asalin jihar.

 

To sai dai kwanaki kadan bayan kalaman na Ganduje, an jiyo Kwankwaso na cewar duk wanda ya sake ya nuna masa adawar siyasa a zaben 2023 dake tafe to tabbas watarana zaiyi dana sanin yin haka.

 

Kwankwaso yace duk wanda ya san shi yasan cewa idan ya samu nasara a zaben dake tafe na zama shugaban kasa, jihar Kano da Arewacin Najeriya dama kasar baki daya zasu amfana.

Latest stories

Related stories

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...