Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiLabaran KanoRundunar Yan sanda zata tabbatar da tsaro yayin ziyarar Remi Tinubu Kano

Rundunar Yan sanda zata tabbatar da tsaro yayin ziyarar Remi Tinubu Kano

Date:

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kara nanata cewa ta shirya tsaf wajen tabbatar da tsaro yayin ziyarar da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu za ta kawo jiharnan a ranar Litinin mai zuwa.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Usaini Gumek ne ya bayar da tabbacin a yau Asabar, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa tuni aka samar da jami’an tsaro domin sanya idanu wajen tabbatar da tsaron.

CP Gumel ya kara da cewa tuni suka mika bayanan duk wuraren da ake sa ran uwargidan shugaban za ta ziyarta ga jami’an da ke da alhakin kai-kawo a wuraren domin inganta tsaron.

Ya shawarci jagororin siyasa da su gargadi magoya bayansu su yi watsi da duk wani abu da ka iya kawo barazanar tsaro yayin ziyarar maid akin shugaban kasar, tare da jan kunnen a shirye su ke wajen dakile duk wata barazanar tsaro yayin ziyarar.

Latest stories

Related stories

Nan da mako biyu za a fara jigilar maniyyatan jihar Kebbi.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...