Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Thursday, April 11, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoShirin AGILE a Kano zai hada hannu da masu ruwa da tsaki...

Shirin AGILE a Kano zai hada hannu da masu ruwa da tsaki a Makoda domin ci gaba da inganta Ayyuka

Date:

Shirin AGILE a jihar Kano zai ci gaba da shigo da masu ruwa da tsaki domin sake bunkasa shirin ta hanyar amfanar da al’ummar birni da kuma karka.

Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da tawagar shirin na AGILE ta kai karamar hukumar Makoda a nan Kano, domin ganawa da masu ruwa da tsaki don sake nuna muhimmancin hadin gwiwa wajen bunkasa shirin ayyukan shirin.

Matakin na zuwa ne domin shigar da masu ruwa da tsaki na cikin gida, musamman shugabannin al’umma, da jami’an gwamnati, Sarakuna da kuma Malamai duka domin sake bunkasa Shirin.

Ana saran Wannan hanya za ta haɓaka ci gaba Da bayyana gaskiya, haɗa kai, da fahimtar alaka tsakanin masu ruwa da tsaki, tare da haɓaka tasirin ayyukan shirin a ko ina.

Bugu da kari, yin cudanya da masu ruwa da tsaki na bai wa shirin AGILE a Kano damar yin amfani da ilimin cikin gida da gogewa, wanda zai kai ga samar da ingantacciyar shawara da kyakkyawan sakamako ga al’umma.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories