Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Wednesday, May 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZa mu Hada Kai Da Premier Radio Don Aiki Tare - Majalisar...

Za mu Hada Kai Da Premier Radio Don Aiki Tare – Majalisar dokokin Kano

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Majalisar dokokin Kano ta nemi haɗin kan Premier Radio don ƙara ƙarfafa alaƙar aiki domin cigaban dimukuradiya a fadin jihar dama kasa baki daya.

Shugaban majalisar dokokin Kano Jibril Isma’il Falgore, ne ya nemi wannan bukata yayin ziyarar da tawagar sa ta kawo Premier Radio a Alhamis din nan.

Shugaban majalisar dokokin Jibril Falgore, da mai magana da yawunsa Kamaluddeen Sani Shawai, yayi jawabi a madadin sa, ya ce majalisar dokokin Kano a shirye take wajen baiwa kafofin yada labarai gudunmawa don cigaban jihar Kano.

Falgore ya kuma yaba da irin gudunmawar da Premier Radio ke bayarwa wajen fito da aikace aikacen majalisa.

A nasa jawabin babban mataimakawa shugaban majalisar dokokin kan sha’anin mulki da harkokin majalisa kuma tsohon Akawun majalisar Malam Abdullahi Alfa, ya ce ziyarar wani bangare ne na nuna godiya bisa gudunmawar da Premier Radio ke bayarwa.

Ya ce daga sanda aka bude Premier Radio kasa da shekaru biyu ta kawo cigaba ta hanyar fito da bukatun al’ummar jihar Kano tare da haskawa gwamnati.

Da yake jawabi, Muhammad Aminu Jolly, Shugaban sashen kasuwanci da gudanarwa ya jaddada kudirin Premier Radio na cigaba da kawo shirye shirye da zasu ciyar da al’umma gaba.

Majlisar dokokin Kanon ta kuma jaddada bukatar kyautata alaka da Premier Radio kan wayar da kan alumma dangane da aikace aikacen ta.

Latest stories

Related stories