Saurari premier Radio
41.1 C
Kano
Monday, April 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn kwafi sanya hannun tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, inda aka sace...

An kwafi sanya hannun tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, inda aka sace Dala miliyan 6.2 daga babban bankin kasa CBN

Date:

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce wasu sun kwafi sanya hannun tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, in da suka cire sama da Dala miliyan 6 da dubu 200 daga babban bankin kasa CBN.

Da ya ke bayyana haka a gaban wata babbar kotu da ke Abuja, Boss Mustapha ya ce bai san batun wata takarda da tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya yi amfani da ita wajen biyan kudaden ga masu sanya ido na kasashen waje a zaben shekarar 2023.

Tsohon sakataren gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a karar da ake tuhumar mista Emefiele, ya ce a tsawon shekarun da ya yi yana rike da wannan mukamin ba shi da masaniya kan takardar.

Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa ta fito ba kuma ba daga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

Tsohon sakatren gwamnatin tarayyar ya kuma shaida wa kotun cewa babu ruwan gwamnatinsu da biyan masu sa ido na kasashen wajen kudade.

Ana dai zargin tsohon gwamnan babban bankin na CBN da amfani da sa hannu na jabu domin karbar kuɗaɗen ba bisa ka’ida ba.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...