Saurari premier Radio
40.8 C
Kano
Monday, April 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTarihin Fitaccen Dan Kasuwa Aliko Dangote

Tarihin Fitaccen Dan Kasuwa Aliko Dangote

Date:

Abun alfahari ne a samu mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afirka ya zama Bahaushe, Musulmi ɗan Arewacin Najeriya kuma dan asalin Jihar Kano.

Wannan mutum da Allah Ya dauka daga cikin Kanawa, Yayi masa Kyauta da arziki shigen na Karuna, shine, Alhaji Aliko Dangote wanda shekara da shekaru har ya zuwa yau ya ke rike da kambun zama na daya a jerin masu arzikin da suka fi kowa kudi a Afirka.

Sana’ar sa ta kasuwancin da yasa gaba, ta kaishi da gina wasu kamfanoni guda 4 da duk Afirka babu kamar su a girma da bunkasa.

Na farko, kamfani ne, na yin siminti da ake kira Dangote Cement, wanda a Najeriya kadai ya ke fitar da kusan rabin simintin da duka kasar nan ta ke bukata a kowace shekara kuma a yanzu wannan kamfani na Dangote Cement ya fadada, ya mamaye fadin kasar nan har ma da wasu kashashen na ketare irinsu Tanzania da Habasha da Congo Brazzaville da Kamaru da Cote d’Ivoire da Benin da Ghana da Zambia da Afruka ta kudu da kuma kasar Togo.

Kamfani na biyu da ya zama abin azo a gani shine na tace danyan mai watau Dangote Refinery da ke Legas. Wannan Kamfani shima dai babu kamar sa a dük Afirka kuma a duniya ma gaba daya, shine na 7 a girma da ingantattun kayan aiki.

Wannan matata sai wanda ya ganta. An kashe dola biliyan 19 ana gına ta. Gari ne guda, kuma a cikin ta bayan yin kananzir da petur da disil da jet oil na jirgin sama, har da sashen yin takin zamanin da babu kamar sa a kasar nan. Wani kaya sai Amale.

Kamfani na uku shine Kamfanin Sukari na Dangote.
A Kano da Nijeriya da ma Afrika, a yau Kamfanin Sukari na Dangote Group na da rinjaye a kan kowane kamfani a kasuwar sukuri, haka kuma, shi ke samar da kashi 70 na kasuwancin sikari da akeyi a Najeriya dun gurungun.

Alhaji Aliko Dangote ne ke da Matatar sukari wadda itace matata mafi girma a Afrika, kuma matata ta uku mafi girma a duniya, tana samar da Tan 800, 000 na sukari a duk shekara.

Sai kuma kamfani na uku wato Kamfanin Dangote Group wanda aka kafa a 1977 kuma wanda yake shine jirgi sha kaya, don ya mallaki masana’antu daban daban kamar masana’antar gishiri a Legas da ta fulawa, a Kano da Kalaba da Legas da na yin Taliya da Buhunhuna a Legas da kuma babban Kamfani mai futar da shinkafa da kifi da taki da futar da auduga da goro da koko da irin sesame da ginger zuwa ƙasashen waje.
Dangote Group yana da hannun jari a cikin gidaje, bankuna, kamfanonin sufuri, masaku, danyan mai, da dai sauran su.
A bangaren sufuri, Dangote a shekarar 2007 yana da Tireloli guda dubu biyu, amma a shekarar 2023 ance akalla Dangote na da Tireloli sama da dubu goma sha biyu (12,000).

Ga kuma jirgin ruwa wanda ke zirga-zirgar daukar kaya da mutane tsakanin kasa da kasa.

An haifi Alhaji Aliku Dangote a ranar 10 ga watan Afrilu, shekara ta 1957 a birnin Kano sunan mahaifinsa malam Muhammad Dangote mahaifiyarsa kuma malama Mariya Sanusi Dantata dukkanninsu sanannu ne. Mahaifinsa, Alh. Muhammadu Dangode shima babban dan kasuwa ne, mahaifiyarsa ɗiya ce ga Sanusi Dantata sananne kuma hamshakin attajiri, dan uwa ga Alh. Aminu Dantata.
Watau dai shi Dangote jika ne ga Alhassan Dantata, wanda shi ma ya taɓa zama attajirin da ya fi kowa kuɗi a Yammacin Afirika a zamanin sa.

Kakan Alhaji Aliko Dangote, watau Alhaji Sunusi Dantata, shi ya sa shi a makarantar Islamiyya, ta Ulumuddeen Islamiyya, inda ya yi karatun AlKur’ani hade da na fikihu.

An sa shi yana dan shekara biyar da haihuwa a duniya.
Daga nan aka tura shi makarantar Boko mai suna “Dantata Memorial Primary School” ta gidan Alhaji Amadu Dantata, bayan nan ya kare a Kuka Primary School.
Aliko Dangote ya fara harkar kasuwanci tun yana dan makarantar firamare inda ya ke zuwa da kwalayen Alewa yana sayarwa Yan ajin su da sauran yaran makarantar. Da ya dan girma, Alhaji Sunusi ya bude musu gidan bulo a Kurnar Asabe, inda suka ci gaba da harkokinsu na buga bulo suna sayarwa har suka kai matsayin da suka tara jari mai dan kauri.
Wannan ita ce sana’ar Alhaji Aliko Dangote ta farko.

Amma fa a zuciyarsa ya fi son ya yi karatu, kasancewar hakan sai Alhaji Aliko ya je ya samu dan’uwansa, yayansa mai suna Alhaji Umar Gote, ya shaida masa abinda yake ciki cewa ya fi son ya yi karatu.
Nan take, Alhaji Umaru Gote ya je gaban Alhaji Sunusi, don rokon a bar Aliko ya karasa karatunsa, amma Alhaji Sunusi ya ki, ya kuma ba shi amsa da cewa “Da Kasuwanci muka budi ido”.
Saboda haka,
Alhaji Aliko suka ci gaba da kasuwancinsu na gidan bulo, shi da Alhaji Nasiru, inda har suka kai ga sayen mota tifa tasu ta kansu, wadda ke yi musu jigilar daukar yashi, idan sun dauko yashi suna kawo wa gidan bulonsu su zuba, ragowar kuwa ana sayarwa da masu bukata.

Bayan rasuwar kakan na sa, Aliko ya sami tafiya government secondary school ta Birninkudu kuma a shekara ta 1978 ne ya kammala karatun kwalejin ta Birnin Kudu, daga nan ya wuce makarantar Jami’a ta Al-azhar dake Cairo inda ya samu kwalin Digiri a kan Kasuwanci da Gudanarwa.

Da ya dawo daga Alkahira, Alhaji Aliko Dangote ya fadada harkar kasuwancinsa da kwangilar gini, inda ya sami kwangilar gina makarantar Primary a garin Takai, Karamar Hukumar Dawakin Kudu da gina makarantun firamare na (U.P.E) a Karamar Hukumar Birnin Kudu da gidajen gajiyayyu na Mariri.
Alhaji Aliko ya koma Legas inda ya shiga harkar sai da siminti a karkashin kawunsa mai suna Alhaji Usman Dantata wanda aka fi sani da suna “Amaka”
Yana zamansa a Legas ya rika odar manyan motoci daga kasar Amurka, inda ya samu wani dan lokaci mai tsawo yana kan wannan harka ta shigo da motoci.
Bayan nan sai Alhaji Aliko Dangote, ya koma shigo da kayayyaki irin su; Sukari da shinkafa da fulawa da kifi da tayoyi da batira, bayan shigo da kayayyaki kuma yana fitar da kayayyaki kamar su; Koko da Karo da Kashu.

Da jarin sa ya karu, Sai Aliko ya shiga gina masana’antu inda ya gina masaka mai suna M.T.N a Ikeja.
Daga nan sai ya sayi wani hannun jari a kamfanin gishiri na tarayyar Najeriya a Ogun State (Ota), wanda yanzu wannan kamfani ya zama mallakarsa.

Alhaji Aliko Dangote ya kuma kafa bankin kasuwanci mai suna “Liberty Merchant Bank” wanda daga baya ya sai da shi da kyakkyawar riba.

A wannan kasa tamu, Najeriya dai, a yanzu, a iya cewa duk dan kasa yana amfana da kayan kamfanin “DANGOTE” imma ta abinci ko abin sha, ko na girki ko bangaren gini, ba shakka wannan ludufi ne ga al’umma.

Wani buri da Alhaji Aliko bai samu ya çıka ba shine na sayen ƙungiyar kwallon ƙafar Arsenal ta ƙasar Burtaniyya inda ya bayyana wannan aniya ta shi a shekarar 2021. Wannan buri nashi dai har yanzu bai samu kammaluwa ba.
Haka kuma Katafariyar Matatar Mai ta Dangote Refinery itama dai a yanzu kamar tana ciwa Dangote tuwo a Kwarya.

An daga bude wannan matata sau uku kuma har yanzu ana ta fafituka don ta fara aiki kamar yadda aka tsara.

Idan aka shawo kan matsalolin da suka jawo mata tsaiko babu shakka za a jinjinawa Dangote saboda jajircewar sa da jarumtakar sa da kishin kasa da ya nuna da kuma hangen nesa.

Irin wadannan halaye su suka sa Aliko Dangote ya sami Kyaututtuka da karramawa
da dama a baya.

Ga kadan daga cikin su:

*Dangote ya samu lambar yabo ta biyu mafi girma a Najeriya, Grand Commander of the Order of the Niger (GCON) daga tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

*Shekaru shida a jere, daga 2013, zuwa 2018 Forbes ta lissafa shi a matsayin “Mutumin da ya fi kowa karfin Arziki a Afirka”.
*A cikin shekara ta 2014, CNBC ta saka shi a jerin “Manyan yan Kasuwa 25 a Duniya” waɗanda suka canza kuma suka tsara ƙarni.

*A cikin Afrilu 2014, mujallar Time ta jera shi a cikin mutane 100 mafiya tasiri a duniya.

*Haka suma Kasuwannin Bloomberg, a cikin Oktoba 2015, sun saka Dangote cikin jerin “mutane 50 Mafi Tasiri a Duniya”

*Dangote Ya lashe “The Guardian Man of the Year” a 2015”.
*Sannan kuma ya lashe lambar yabo ta 2016 wato Jagoran Kasuwancin Afirka, wanda Cibiyar Afirka-Amurka (AAI) ta shirya.

*mujallar New African a shekarar 2015, da kuma 2017, da 2018 da kuma shekarar 2019.ta zabe shi “wanda yafi kowa tasiri da gina Afirka.”
*Fitaccen mai ba da taimako a nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya samu lambar yabo ta Lifetime Achievement Award daga kungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya (NECA), kungiyar masu daukar ma’aikata a kamfanoni masu zaman kansu a kasar nan.

*A shekara ta 2023 An karrama Dangote Industries Limited da lambar yabo ta shekarar da ta gabata, domin karamawa da kwazon da kamfanin ya yi a cikin shekarar da ta gabata.

*A wannan shekarar da muke ciki ne shugaban kasar Sanigal ya karrama Alhaji Aliko Dangote da lambar kasar da tafi kowacce girma.
Don mahimmanci Wannan lambar sai da shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya taya Alhaji Aliko Dangote murnar karramawar da shugaban kasar na Senegal ya ba shi.

Kyautar ita ce tsari mafi girma a Senegal kuma an bada kyautar ga babban dan kasuwa a ranar 2 ga Fabrairu.

An shaida cewa Alhaji Aliko Dangote mutum ne mai saukin kai kuma mai biyayya ga iyayensa musamman ga mahaifiyarsa, da itace kawai ta ke raye.

Wadanda suka san shi sunce yana bin mahaifiyarsa sau da kafa. Kuma yana biyayya ga ‘yan’uwan iyayensa kamar su Alh. Aminu Dantata, yana kuma girmama yayyensa da abokan hurda.
Hajiya Mariya mahaifiyar Alhaji Aliko Dangote, ta kasance mai yawan hidima ga gajiyayyu, mai yawan hidima ga al’umma, mai taimakon Musulmi da Addinin Musulunci.

A yanzu dai Alhaji Aliko Dangote yana da shekaru 67 a duniya, ya taɓa aure sau biyu amma sun rabu da matayensa. Yana da ‘ya’ya uku: Mariya Aliko Dangote da Halima Aliko Dangote da Fatima Aliko Dangote.

Muna yi wa Alhaji Aliko fatan alheri da addu’ar Allah Ya kara inganta rayuwar sa da dukiyar sa.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories