Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiEFCC tana neman matar tsohon Gwamnan CBN da wasu mutum 3 bisa...

EFCC tana neman matar tsohon Gwamnan CBN da wasu mutum 3 bisa zargin almundahana

Date:

Hukumar EFCC tana neman matar tsohon Gwamnan CBN Margaret Dumbiri Emefiele da wasu mutum 3 bisa zargin almundahana.

Mutum ukun su hada da Eric Ocheme Odoh, Jonathan Omoile, da Anita Joy Omoile. EFCC tana zargin mutum hudun sun hada baki da tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele wajen karkatar da wasu makudan kudade mallakar gwamnatin tarayya.

Laifukan da ake zarginsu dashi sun hada da samun kudi ta hanyar zamba, sata hadi da sabawa sashe na 411, 287, da 314 na dokokin jihar Legas.

Hukumar ta bukaci dukkan wanda yake da bayani game da wadannan mutane su tuntubi kowane ofishin EFCC ko kuma su kira lambar 08093322644.

Wannan sanarwar na zuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’ar da Godwin Emefiele, wanda ke fuskantar tuhumar damfara da karkatar da Naira biliyan 1.8 da dala miliyan 6.2.

Hakazalika ana tuhumar Emefiele da fifita matarsa da sirikinsa ta hanyar ba su kwangilar gyaran gidan Gwamnan CBN da ke Legas wanda ya saba da doka.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...