Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano za ta fara kai samame rumbunan da yan kasuwa ke...

Gwamnatin Kano za ta fara kai samame rumbunan da yan kasuwa ke boye kayan abinci

Date:

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara wani shirin bincikar yan kasuwa dake boye kayan abinci.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce sun gano cewa boye kayan na daga cikin abubuwan da suke kara tsadar kayan masarufi a jihar Kano.

Ya kuma ce bayan korafe-korafen da Hukumar ta karba daga mutanen Kano ta umarci jami’anta su fara bincike a duk wuraren da ake zargin an boye kayan abincin.

Muhuyi ya ce sun fara aikin zagaye domin zakulo irin wadannan yan kasuwa inda ya ce duk mutumin da suka kama to zai dandana kudarsa.

“Farashin sukari a halin yanzu yah aura naira 73,000, abin takaici ne sosai. Na ziyarci kasuwannin da ake sayar da shinkafa a Kano jiya Alhamis, inda muka gano cewa ana sayar da kilo 50 na shinkafa akan Naira 58,000”

Ana dai ta zarge-zarge cewa manyan yan kasuwa na boye kayan masarufi har sai ya yi tsada su fito da shi su sayar, abinda ake ganin yana kara dagula lamarin tsadar kayan na masarufi.

Sai dai yan kasuwar na musanta zarge-zargen da ake yi musu.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan kasuwar da ke da ɗabi’ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawan ƙasar ke cikin matsin rayuwa.

Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da ‘yan ƙasar ke ciki.

Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.

”Ma’aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau’in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa ‘yan ƙasar nan ba da jimawa ba”, in ji ministan.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa faɗin ƙasar na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magan da su sun kuma amnce za su fito da metric ton 60,000, don a sayar wa ‘yan ƙasar.

Ministan ya ce idan ta kama ma ƙasar za ta ya shigo da abinci daga ƙasashen wajen do magance matsalar tsadar abincin a faɗin ƙasar.

”Nan gaba kaɗan za a yi haka idan ta kama a yi”, in ji Muhammad Idris.

Ministan ya kuma gargaɗi masu ɓoye kayan abinci da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya.

”Ba abu ba ne na alkairi ana cikin wannan matsatsi, kai kuma ka je ka ɓoye abinci don wata manufa taka da daban, don haka gwamnati ke kira ga irin waɗanan ‘yan kasuwa da su fito da waɗanan kayayyaki domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa”, in ji ministan.

Yana mai cewa duk ɗan kasuwar da ya ki bin wanan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu.

Latest stories

Related stories