Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBayan watanni 8 da harin gidan yarin kuje akwai fursunoni 460 da...

Bayan watanni 8 da harin gidan yarin kuje akwai fursunoni 460 da ba a maidasu sarka ba

Date:

Watanni 8 bayan kai hari ga gidan yarin kuje dake Abuja, rahotanni na cewa har kawo yanzu akwai fursunoni 460 da suka tsere ba tare da an kamasu ba.

Jaridar the punch ta gano bayanan fursunonin a ranar juma’a ta hannun hukumar kula da gidajen yari ta kasa.

Idan za’a Iya tunawa dai an kai harin gidan yarin na Kuje a ranar 5 ga watan yulin a shekarar 2022, abinda yayi sanadiyyar tserewar fursunoni da dama cikinsu har da yan ta’addar boko haram 64.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewar an samu damar sake kama mutane 421 da suka tsere, Inda aka watsa bayanan sauran fursunonin da ba’a samu nasarar kamawa ba ga yan sandan dake kula da yan ta’adda na duniya.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...