Saurari premier Radio
26.3 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSojoji sun kashe Yan Ta'adda biyar a Kaduna

Sojoji sun kashe Yan Ta’adda biyar a Kaduna

Date:

Sojoji a jihar Kaduna sun kai sumame wani daji da ‘yan ta’adda ke zaune, inda suka kashe mutum 5.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojan Najeriya ta 1, Laftanar Kanar Musa Yahaya, ne ya bayyana haka a Wata sanarwa da ya fitar.

Yace “An kashe ‘yan ta’addan 5 ne a wani samame da aka kai a hanyar Kanti-Tantatu da ke dajin Kubusu da kuma yankin tudun Kaso a karamar hukumar Chikun ta jihar. Sojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK 47 guda hudu, mujallu AK 47 guda shida, bindiga  24 kirar 7.62mm, babura uku, adda guda daya, wayar hannu biyu da wasu layu na tsafi”

Babban kwamandan runduna ta daya  kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Whirl Punch Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana gamsuwa da yadda sojojin ke gudanar da ayyukansu tare da yabawa jajircewarsu a yayin aikin.

Ya kuma bukaci dukkan ‘yan kasa masu bin doka da oda da su ci gaba da tallafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro da sahihan bayanai masu inganci da za su taimaka wajen yaki da masu aikata laifuka.”

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...