Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan bindiga sun kashe mutum 15 a Taraba

Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Taraba

Date:

Wasu ‘yan bindiga kimanin 60 sun kai farmaki kauyen Garin Baka da ke karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba inda suka kashe akalla mutane 15.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa kauyen da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Juma’a inda suka yi ta harbe-harbe a wurare daban-daban.

Yan bindigar sun kona gidaje tare da satar shanu da wawashe shaguna da rumbun ajiya.

Wani mazaunin garin, Yakubu Garba, ya shaidawa manema labarai a lokacin da maharan suka zo, da yawa daga cikin mutanen kauyen na yin sallah a cikin wani masallaci.

Garba ya ce wasu daga cikin mazauna garin sun tsere zuwa cikin dajin da ke kusa da wurin, amma wasu daga cikin iyalansa na daga cikin wadanda aka kashe a harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin amma bai iya bayyana ainihin adadin wadanda aka kashe ba. A cewar sa, ana jiran rahoto a hukumance daga sashin ‘yan sanda na Sunkani wanda ke kula da yankin.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...