Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon magatakardan hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa wato JAMB.
Sabon shugaban hukumar zai maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa’adinsa na biyu zai ƙare a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2026 bayan shekaru da dama yana jagorantar hukumar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana Farfesa Aina a matsayin ƙwararren masani a fannin tsarin na’urorin zamani da harkokin gudanar da jarabawa, wanda yake da gogewa sosai a ɓangaren fasahar zamani da gyaran hukumomin gwamnati.
An bayyana cewa Aina ya karanci fannin Computer Systems Engineering a jami’ar Kent da ke Birtaniya, inda ya samu digirinsa na farko kafin ya yi digiri na biyu da digirin-digirgir a jami’ar Loughborough University.
Haka kuma ya halarci shirin horaswa na manyan jami’an gudanarwa a makarantar Lagos Business School domin ƙara ƙwarewa a harkokin shugabanci da tafiyar da hukumomi.
Farfesa Aina malami ne a sashen koyar da ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa Computer Engineering na jami’ar Obafemi Awolowo University da ke Ile-Ife, kuma ya fara hulɗarsa da JAMB tun lokacin yana bautar ƙasa.
Sanarwar ta ce gogewar da ya samu tun daga lokacin ta taimaka wajen fahimtar tsarin gudanar da jarabawa da amfani da bayanai wajen inganta tsarin shiga jami’o’i a Nijeriya.
An kuma bayyana cewa sabon shugaban na hukumar JAMB mamba ne a ƙungiyoyi da dama na ƙwararrun injiniyoyi ciki har da Council for the Regulation of Engineering in Nigeria da Nigerian Society of Engineers da kuma Institute of Electrical and Electronics Engineers.
Fadar shugaban ƙasa ta ce ana sa ran Farfesa Aina zai yi anfani da gogewarsa wajen ɗora hukumar JAMB a kan nasarorin da tsohon shugaban hukumar Farfesa Oloyede ya samar tare da ƙara inganta tsarin gudanar da jarabawa a Nijeriya.
