Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sha alwashin ɗaukar matakan da za su inganta ayyukan gidan talabijin na Abubakar Rimi Television, ARTV, domin ya samu damar yin gogayya da sauran kafafen yaɗa labarai a faɗin ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Daraktar Labarai da Al’amuran Yau da Kullum ta ARTV, Husaina Sa’id Bichi, ta fitar.
Rahoton ya ce Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Sa’ad Aminu Sa’ad Ungogo, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da mahukuntan ARTV.
Ya ce majalisar za ta goyi bayan dukkan matakan da za su taimaka wajen inganta ayyukan tashar.
Sa’ad Aminu Sa’ad Ungogo ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta samar wa tashar kayan aikin yaɗa labarai na zamani, inganta gine-ginenta da kuma ƙarfafa ƙwarewar ma’aikatanta.
A nata bangaren, Shugabar ARTV, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim, wadda mataimakinta Alhaji Idris Abba ya wakilta, ta tabbatar da aniyar tashar na ci gaba da samar da ingantattun shirye-shirye masu ilmantarwa da nishaɗantarwa ga al’umma.
