Rahotanni na nuna cewa kuɗin ajiyar Najeriya dake waje sun kai dala biliyan 53.11, matakin da ya zama mafi girma da ƙasar ta samu cikin sama da shekaru 17.
Bayanan Babban Bankin Najeriya CBN sun nuna cewa ajiyar kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 53.11 zuwa ranar 24 ga Agusta, 2026.
Wannan adadi shi ne mafi kusa da matakin da Najeriya ta taɓa samu a Janairu 2009, lokacin da ajiyar kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 53.25.
Bayanan sun nuna cewa a ranar 3 ga Yuni, adadin bai wuce dala biliyan 49.96, kafin ya ƙaru zuwa dala biliyan 53.11 a ranar 24 ga Agusta.
Hakan na nufin ajiyar ta ƙaru da kusan dala biliyan 3.15 cikin wannan lokacin.
Ƙarin kuɗaɗen shiga daga fitar da ɗanyen man fetur, da kuma ƙarin shigar daloli cikin tattalin arzikin ƙasar, na daga cikin abubuwan da ake ganin sun taimaka wajen wannan ƙaruwar.
Masana tattalin arziƙi na cewa ƙarin ajiyar kuɗin waje na ƙara wa Najeriya ƙarfin tunkarar matsalolin tattalin arziƙin duniya, musamman matsin lambar da ake fuskanta a kasuwar canjin kuɗi.
Sai dai sun yi gargaɗin cewa babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da dorewar wannan ƙaruwa, ta yadda ajiyar ba za ta dogara kacokan kan abubuwan da ka iya sauyawa ko gushewa cikin ɗan lokaci ba.
Ƙarin ajiyar kuɗaɗen waje ya zo ne a daidai lokacin da CBN ke ci gaba da aiwatar da manufofin kuɗi da nufin dakile hauhawar farashin kayayyaki da kuma inganta yanayin tattalin arziƙin ƙasar.
Masana sun ce idan aka ci gaba da samun ƙarin shigar kuɗaɗen waje tare da ingantaccen tsarin sarrafa su, hakan na iya ƙara ƙarfafa darajar Naira da kuma samar da wani mataki na kariya ga tattalin arziƙin Najeriya daga matsalolin da ka iya tasowa daga kasuwannin duniya.
