Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu tambaya kan dalilin da ya sa ’yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar tsadar rayuwa, bayan shafe kusan shekaru uku da gwamnatin Tinubu ta fara gudanar da mulki.
Atiku ya yi amfani da misalin da shugaba Tinubu ya yi a baya na kwatanta Najeriya da mara lafiyar da ke fama da cutar kansa, yana mai tambayar dalilin da ya sa ’yan Najeriya ke ci gaba da shan wahalar sayen abinci, magunguna da kuma kuɗin sufuri zuwa wuraren aikinsu.
A cewar Atiku, halin da jama’a ke ciki ya nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta ƙara mayar da hankali kan rage matsin tattalin arzikin da talakawa ke fuskanta.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya, musamman wajen samun abinci, kiwon lafiya da sufuri.
Kalaman Atiku na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu da kuma yadda suke shafar rayuwar ’yan Najeriya, a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
